climate change
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kokarin cimma yarjejeniya kan sauyin yanayi

A yau da rana ne za a gabatar da wani daftarin yarjejeniyar da aka cimma a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Paris.

Hakan zai sa mu fahimci irin tasirin da yarjejeniyar za ta yi, kuma kasashen da suke halartar taron za su shafe kwanaki biyu don rarraba aikin da ya kamata kowacce kasa ta yi. Kasar da ta fi fuskantar matsalar sauyin yanayi dai ita ce Namibia.

Tana fama da matsanancin fari, kuma ana tunanin yanayin kasar wadda take kudancin Afrika zai kara munana nan da shekaru 10.