Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Fada ya barke a jamhuriyar Afirka ta tsakiya

Mummunan fada ya barke a unguwar musulmi dake Bangui yayin da ake gudanar da kuri'ar raba gardama a kasar.

Rahotanni na cewa, an yi amfani da manyan makamai da roka yayin arangama tsakanin magoya baya, da kuma masu adawa da kudin tsarin mulkin kasar.

Har yanzu dai babu cikakken bayani dangane da asarar rayuka, amma rahotanni na cewa, mutane da dama sun jikkata.

Tuni aka aika dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya domin su kwantar da hankulla.

A unguwar Kaga-Bandoro an dakatar da jefa kuri'a bayan an bankawa akwatin zabe da kuma takardun jefa kuri'a wuta.

Jamhuriyar Afirka ta tsakiya dai ta kasance cikin rikici tun daga lokacin da ta samu 'yan ci daga Turawan Faransa.