Garin da mata zalla ke rayuwa

Wakiliyar BBC Laeila Adjovi ta ziyarci garin Beguedo da ke Burkina Faso, garin da mata kan dauki tsawon shekaru ba su ga mazajensu ba.

Alimata da Nematou
Bayanan hoto,

Akwai wani gari a yammacin Afrika inda ya zama ala’da ga maza su tafi har Italiya don neman rufin asirin rayuwa. A kan dai bar matan su kadai a garin na tsawon shekaru. Amma ba a garin Beguedo kawai irin wannan al’amari ke faruwa ba, akwai wasu garuruwa ma da ake irin wannan al’ada a nahiyar Afrika., inda maza ke tafiya ci-rani kasashen Turai don neman gwaggwaban aiki.

Bayanan hoto,

Alimata Bara wata mace ce mai yawan fara'a da barkwanci. Amma a yau tana yi wa kanta dariya saboda rashin sa'arta na wadda ta manta rabonta da yin kwanciyar aure da mijinta.

Bayanan hoto,

Ta yi aure shekaru bakwai da suka gabata lokacin tana da shekara 17. ta auri wani da ke zuwa dan ci-rani a Italiya.

Bayanan hoto,

Ta ce "Zan iya tunawa a kasuwa na hadu da shi, sai muka fara zance. Daga nan sai ya kawo wa iyayena goro. Cikin kwanaki 10 kacal sai muka yi aure."

Bayanan hoto,

Tun bayan aurenta, watanni shida kacal ta yi tare da mijinta. Tana da 'ya daya mai suna Omayma 'yar shekara shida. Dansu na biyu kuwa mai suna Obaidou dan shekara uku, sau daya ya taba ganin babansa.

Bayanan hoto,

Omayma na jin dadi a duk lokacin da aka bata album din hotuna tana kallon hoton babanta, tare da nuna shi tana kiran "Baba."

Bayanan hoto,

A garin Beguedo dai mai nisan kilomita 230 daga Ougadougou babban birnin Burkina Faso, mata da yawa suna cikin irin halin da Alimata ke ciki ne. Nematou makwabciyar Alimata ce, ta auri dan uwan Saada mijin Alimata, wanda shi ma yake ci-rani a kasar waje.

Bayanan hoto,

Nematou da Alimata kusan sa'anni ne, kuma sun matukar shakuwa da juna, suna tattauna matsalolinsu na wahalar da ke tattare da kula da yaransu. Wata tsohuwar mai rike da mukamin magajin gari Beatrice Bara, ta ce rabin matan wannan kauye duk mazajensu sun tafi ci-rani sun bar su.

Bayanan hoto,

Lokacin da Alimata ta auri Saada a shekarar 2008, ta zaci ba da dadewa ba za ta iske shi a Italiya. "Ya ce da zan je na iske shi a can, amma kuma sai ya rasa aikinsa," a cewar Alimata.

Bayanan hoto,

Kazalika, yayin da Saadaya samu damar ginawa Alimata gida mai daki daya a kusa da gidan iyayensa, bai taba samun tagomashi sosai ba a Italiya balle ya turo kudi masu yawa gida. Yana iya tura fam 25 ne kacal cikin watanni.

Bayanan hoto,

Ta yi sa'a bata dogara kacokam kan abinda Saada ke aikowa. Ta fara karamar sana'a ta sayar da gawayi. Tana kuma sayar da wani ab daga cikin amfanin gonar da ta noma, kuma ta haka ne take biyawa kanta bukatu.