boko
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan kunar bakin wake sun hallaka kansu a Borno

Rahotanni daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno na cewa, wasu daga cikin 'yan mata 'yan kunar bakin wake biyar da suka yi yunkurin shiga Maiduguri ta hanyar Mafa sun halaka kansu.

Harin kuma ya janyo mutuwar wasu 'yan sintirin tsaro na sa kai, watau Civilian JTF.

Alhaji Muhammed Kanar, shi ne jami'an hukumar agajin gaggawa ta NEMA a jihohin arewa maso gabas.

Ta waya ya yi wa Isa Sanusi karin bayani akan abinda ya faru: