An mayar da rajistar jirage maras matuki intanet

Gwamnatin Amurka ta mayar da rajistar jirage marasa matuki kai tsaye ta intanet.

Wasu sabbin ka'idoji na rajistar jirage marasa matuki ta shardanta cewa duk wanda ya kai shekara 13 da haihuwa ko sama, ya kuma mallaki jirgi maras matuki da ya bayar da cikakken bayani game da kansa.

Ka'idar rajistar ta tanadi cewa duk wanda ya mallaki jirgin maras matuki bayan 21 ga watan Disamba dole ne ya yi rajista da hukumar kula sufurin jiragen sama ta kasar kafin ya fara sakin jirgin a karon farko a sararin samaniya.

An ba wadanda suka dade da mallakar jirgin zuwa 19 ga watan Fabarairu da su yi tasu rajistar a intanet, wanda duk ya ki za a ci shi tara mai yawa.

Wadanda suka yi rajistar za a ba su wata lamba wacce za su lika a jikin jirgin.

Tsawon wa'adin rajistar shekaru biyu ne.

Gwamnati ta yafe dala 5 ga kwanaki 30 a aiki da tsarin domin karfafawa mutane gwiwa da su yi rajistar, wadanda kuma suka yi kunnen kashi za a ci su tarar da ta kai kimanin dala 27,500.

Gwamnati ta fito da tsarin rajistar ne sakamakon yawan kutsen da jiragen su ke yi a kebabbun wurare da inda bai kamata jiragen su yi shawagi ba, kamar kusa da filayen tashi da jiragen sama, da wuraren cinkoson jama'a da kuma wuraren da jiragen ka iya kawo cikas ga ayyukan gaggawa.

Hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta ce ta matsa da rajistar ne kafin bukukuwan Kirsimeti a inda ake zaton yawan jiragen zai karu sakamakon rarraba su da za'a a iya yi a matsayin kyauta.

Hukumar ta sa dokar cewa masu jiragen dole ne su kayyade shawagin su zuwa mita 120 ko kafa 400.

Dole ne mai sarrafa jiragin ya kasance ya na ganin jirgin yayin da yake shawagi, kar kuma ya yi shawagi kusa da jiragen sama na ainihi, kar kuma jirgin ya yi shawagi a inda cincirindon jama'a su ke, kamar filin wasa ko kuma inda ake wani wasan motsa jiki, da kuma kusa da inda ake gudanar da ayyukan ceto.