Yadda za ka zauna lafiya da kwamfutarka a lokacin Kirisimeti

Image caption Kiyaye yadda za ka yi amfani da kwamfutarka zai sa ka zauna lafiya a lokacin hutun Krisimeti

Wani masanin kwamfuta Scot Culp, ya rubuta wata makala mai muhimmancin a kan tsaron na'urar kwamfuta, inda ya bayar da wasu shawarwari a kan yadda mutane za su zauna lafiya da kwamfutarsu.

Masanin ya kira makalar da suna muhimman shawarwari 10 game da tsaron kwamfuta a lokacin bukukuwan kirsimeti a shekara ta 2000.

Shekaru 15, lokaci ne mai tsawo a batun tsaro a harkar kwamfuta, don haka wannan lokaci na kirsimeti shi ne ya fi dacewa a waiwayi wadannan shawarori kamar haka:

Duba da yanayin cewa za ka iya cin karo da kalubale dangane da tsaro a wannan lokaci na bikin kirsimeti.

Lokacin da yiwuwar kai hari a kwamfuta ke karuwa, kiyaye wadannan shawarwari ka iya sa ka yi biki da kwamfutarka lafiya.

Shawara ta 1: Kar ka yarda wani ya yaudare ka ya sa manhajarsa a kwamfutarka, ta haka masu kutse ke kutsawa cikin kwamfutarka su haifar maka da matsala.

Ta sakon email ko ta wani adireshi ko kuma ta wani rataye a wasikar email wacce idan ka bude sai ta makala maka jangwam.

Shawara ta 2: Kar ka yarda wani ya sauya maka tsarin na'urar kwamfutarka.

Yi hattara da inda ka sayi kwamfutarka, ba lallai ne tana da ingancin da ka ke zato ba.

Ka sayi na'urarka a inda za'a iya ba ka kaya masu inganci da nagarta.

Shawara ta 3: Kar ka ka bar kwamfutarka ta zama ta ci barkatai, watau kowa ya bude ya kuma rufe yadda yaga dama, ya kuma yi abinda ya ga dama da ita.

A dalilin haka wani na iya sa maka wani abu ko da kwamfutar tana kashe ne.

Kar dai ka sake ka kyale wani da na'urarka ba tsaro.

In har zai yiwu ka kulle babban rumbun kwamfutarka musamman idan ta na kashe.

Shawara ta 4: kar ka kyale wani ya saka wani abu a shafinka na intanet.

Shawara ta 5: Samar da kalmar sirri mai karfi.

Yi amfani da kalmar sirri mai sarkakiya, yi amfani da haruffa da lambobi a kalmar sirrinka wajen bude kwamfutarka.

Kar kuma ka fadawa kowa kalmar sirrinka, kar kuma ka rubuta a inda wani zai gani.

Shawara ta 6: Mai lura da kwamfutarka ya zama amintacce.

Ka tabbatar da cewa ka tsare muhimman bayanan kwamfutarka da karin matakai ba kawai sassaukar kalmar sirri da suna kawai ba, idan ba kai kadai ka ke amfani da ita ba.

Shawara 7: Ingancin makullin bayanai cikin kwamfuta ya dogara ne a kan ingancin mabudinsa.

Ka adana mabudin kwamfutarka a wurin da ya dace kuma nesa da kai saboda kuskuren wani ya gani.

Shawara ta 8: Ka tabbata ka yi amfani da manhajar kare kwamfutoci daga hadari mai inganci ka kuma rika sabunta manhajar akai-akai

Shawara ta 9: Gara ka yi matukar boye kanka a intanet, duk da cewa sirri yana da kyau. Sai dai komai yayi yawa cuta ne.

Shawara ta 10: Fasahar zamani ba abar dogaro ba ce kacokam!

Ya yi taka tsan-tsan