Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An fitar da sakamakon wucin gadi na zabe a CAR

Sakamakon wucin gado na zaben shugaban kasa a Jumhuriyar Tsakiyar Afrika, ya nuna cewa tsohon pira ministan kasar ne, Faustin Arkanje Twadera, ke kan gaba.

An dai kidaya galibin kuru'u a Bangui, babban birnin kasar. Sai dai akwai alamun zaa je zagaye na biyu a karshen wannan watan. Yan takara 30 ne suka tsaya a zaben, kuma kasar ta shafe shekaru 3 tana fama da rikicin addini.

Ga dai rahoton Jimeh Saleh.