Hotunan tarihin Nigeria kafin juyin mulkin 1966

Hotuna masu cike da tarihi da Baba Shettima ya dauka. Mun wallafa su ne a ranar cika shekaru 50 da juyin mulki na farko a Najeriya watau a ranar 15 ga watan Janairun 2016.

Taron kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyar NCNC da kuma NPC. Shugabannin jam'iyyun Ahmadu Bello, da Tafawa Balewa da Azikwe da Okpara da Ribadu da Okotie-Eboh.
Bayanan hoto,

Taron kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin jam'iyyar NCNC da kuma NPC. Shugabannin jam'iyyun Ahmadu Bello, da Tafawa Balewa da Azikwe da Okpara da Ribadu da Okotie-Eboh.

Bayanan hoto,

Firai minista Abubakar Tafawa Balewa da Micheal Okpara da Cif Stephen Osita Osadebe da Samuel Akintola da Ahmadu Bello a shekarar 1963.

Bayanan hoto,

Birgediya Janar Zakariya Maimalari da Cif Okotie-Eboh da kuma Janar Aguyi-Ironsi a lokacin liyafa a Lagos a shekarar 1966.

Bayanan hoto,

Tsohon shugaban kasa, Nnamdi Azikwe na rantsar da Firai minista, Abubakar Tafawa Balewa a shekarar 1964.

Bayanan hoto,

Firimiya Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto tare da ma'aikatansa A Lemu da kuma M. Attah. Wannan ne hoto na karshe da aka dauke shi kafin a kashe shi.

Bayanan hoto,

Firai Minista Abubakar Tafawa Balewa tare da tsohon shugaban mulkin soja, Aguiyi Ironsi.

Bayanan hoto,

Sa hannun Firai minista, Abubakar Tafawa Balewa.