Hotunan marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa
A ranar 15 ga watan Janairun shekarar 2016 ne ake cika shekara 50 da yin juyin mulkin farko a Najeriya, lamarin da ya yi sanadiyar kisan shugabannin kasar irin su Sir Abubakar Tafawa Balewa. Ga wasu daga cikin hotunansa, wadanda Is'haq Khalid ya dauko.

Sir Abubakar Tafawa Balewa yana da matukar kaunar jama'a, musamman 'ya'yansa, wadanda yake yawan zama tare da su.
Marigayi Firayim Ministan Najeriya bai yi rayuwa irin ta kece-raini ba, shi ya sa ma yake kwanciya a wannan gadon har lokacin da rai ya yi halinsa.
A wannan dakin ne aka adana agoguna da talabijin da ma wasu kayayyaki da Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi amfani da su.
Wadannan suna daga cikin hulunan da Sir Abubakar Tafawa Balewa ya rika sanyawa.
Sir Abubakar Tafawa Balewa shahararren manomi ne, kuma wannan takalmin ruwan da yake yawan sanyawa ne.
An gyara kabarin Sir Abubakar Tafawa Balewa domin mutane su rika tunawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya.