Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shia: Tawagar BBC ta yi tattaki zuwa Zariya

Shaidu sun gaya wa BBC cewa, sojojin Najeriya sun kashe 'yan Shia masu yawan gaske, a harin da suka kai masu a watan Disamba.

In ji kungiyoyin kare hakkin dan adam, daruruwan mutane ne suka hallaka a lokacin artabun a Zaria.

Rundunar sojan ta musanta zargin keta hakkin jama'ar. Wakilinmu Abdullahi Kaura Abubakar ya je Zariyar, ga kuma rahotonsa na musamman: