Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Amnesty ta caccakin sojin Nigeria

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta mayar da Manjo Janar Ahmed Mohammed, daya daga cikin manyan hafsoshin sojin da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta nemi gwamnati ta bincika kan yiwuwar aikata laifukan yaki.

Rundunar sojin ta bayyana haka ne bayan da kungiyar kare hakkin Bil adaman ta yi suka kan yadda aka mayar da Manjo Janar Ahmed Mohammed din a cikin watan Janairu.

Amnesty International ta ce bai dace a mayar da Janar Mohammed aiki ba tare da kwakwarar bincike ba kan zarge-zargen da ake masa.

An dai yi wa Janar din ritaya ne a cikin 2014 bayan wasu sojoji da suka yi bore suka harbe shi a barikin Giwa da ke Maiduguri.

Aminu Abdulkadir ya tuntubi kakakin rundunar sojin Najeriyar Birgediya Janar Rabe Abubakar domin samun bayani kan dalilan rundunar na mayar da kwamandan ba tare da wani bincike kamar yadda kungiyar Amnesty International ta bukata ba