Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An cafke bata-gari 25 a Kaduna

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya, NDLEA shiyyar Kaduna ta ce ta kama wasu masu sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi su 25 a jihar.

Hukumar ta nuna wa manema labarai wasu tarin kwayoyi ciki har da hodar iblis, watau Cocaine da kuma tabar wiwi da ta ce ta kwace su ne daga hannun dillalan kwayoyi a jihar.

Gwamnatin jihar Kaduna dai na cewa a kokarin magance tafka manyan laifuffuka ne ta hada gwiwa da hukumar NDLEA, abin da ya haifar da wannan kame.

Ga rahoton Nurah Mohammed Ringim daga Kaduna.