Za mu murkushe ta'addanci a Nigeria - Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ganin bayan ta'addanci a kasar.

Shugaban ya furta hakan ne a wata hira da Editanmu Mansur Liman a nan London.

To ganin cewa a baya, shugaba Buharin ya dibar wa gwamnatinsa wa'adin karshen watan Disamban bara, na murkushe 'yan Boko Haram, amma har yanzu su na cigaba da kai hare-hare, Mansur din ya tambaye shi: anya kuwa bai yi riga malam masallaci ba wajen cewa sun karya lagwon kungiyar?