Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yajin aikin masu burodi a Najeriya

Masu gidajen burodi a Najeriya sun yi yajin aiki domin nuna damuwarsu da tashin farashin kayayyakin da suke amfani da su na yin burodin da suka hada da alkama da butter da sugar da sauran su.

A Najeriyar dai jama'a da dama a cikin al'umma sun saba amfani da burodin wajen karin kumallo. To ko yaya wannan yajin aikin ya shafe ku?

Kuma menene ma ya jawo tashin farashin kayayyakin da ake amfani da su na yin burodi kuma ina mafita.