Sojojin Nigeria
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Sojojin Nigeria za su koyo dabaru a Colombia

Rundunar sojin kasa ta Nigeria ta ce manufar ziyarar da wasu manyan mukarrabanta suka kai zuwa Colombia shi ne domin su karo ilmin yaki da ta'addanci.

Babban Hafsan Sojin Kasa na Nigeriar Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai shi ne dai ya jagoranci wata tawagar manyan mukarraban sojojin kasa na Nigeriar zuwa wasu manyan cibiyoyin sojin Colombiyan.

Ziyarar na zuwa ne daidai lokacin da sojojin kasa na Nigeriar ke cigaba da fafatawa da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeria.

Colombia dai ta yi fama da 'yan tawaye shekara da shekaru kuma a yanzu ne kasar ke kokarin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da 'yan tawayen na FARC.

Mai magana da yawun sojojin kasa na Nigeria Kanar Sani Usman Kukasheka ya shaidawa BBC cewa za a koyi darasi daga ziyarar