sarki sanusi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Na gamsu da kamun ludayin Buhari - Sarki Sanusi

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi 11, ya bayyana gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wata hira ta musamman da BBC a wata ziyara da ya kai Africa ta Kudu, Muhammadu Sanusi na biyu ya ce, gwamnatin Shugaba Buhari ta yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar Boko Haram, kuma dukkanin wadanann abubuwa ne da za su taimakawa tattalin arzikin kasa.