Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana kafa wa 'yan gudun hijira tantuna a Turkiyya

Ma'aikatan agaji a Turkiyya na cigaba da kakkafa tantuna da kuma rarraba kayan agaji ga dubun dubatar 'yan gudun hijirar Syria da hukumomin Turkiyyar suka hana tsallakawa cikin kasar. Pira ministan Turkiyyar, Ahmet Davutoglu ya ce yanzu haka 'yan gudun hijirar Syria dubu 30 ne ke dannawa zuwa iyakar Turkiyya. Wasu sun nufi birnin Kilis ne na kan iyaka. Da ma dai akwai wasu karin dubu 35 da ke cikin kasar. Ga rahoton Jimeh Saleh.