Tim Cook
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

San Bernadino: Apple ya ce zai daukaka kara

Kamfanin Apple zai kalubalanci wani umurnin kotu na taimakawa hukumomi bude wayar daya daga cikin mutanen da ke da hannu a harbe-harben San Bernadino.

Shugaban Kamfanin na Apple, Tim Cook ya ce idan har kamfanin na Apple zai kiyaye da umurnin, to kuwa dole ya kirkiri wata manhajar da za ta kasance ta yiwu a iya bude dukanin wata wayar da kamfanin yayi.

Yayi gargadin cewar hakan zai yi barazana ga tsaron masu amfani da wayoyinsa da kuma kafa wani mummunan misali.

Ga dai rahoton da Ahmed Abba Abdullahi ya hada mana.