mental health
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Agaji ga masu tabin-hankali a kasar Benin

A ci gaba da rahotannin da mu ke kawo muku a kan mutanen da ke fama da tabin-hankali da kuma hidimar kula da su wanda BBC ke gabatarwa.

Za mu leka jamhuriyar Benin inda ake danganta haduwa da tabin-hankali cewa na zuwa a sakamakon taba kurwa da mayu kan yi wa mutum ko kuma jifa.

A jamhuriyar Benin, wata kungiya ta Saint Camille da Gregorie Ahingbonon dan shekara 65 mai aikin kanikanci ke jagoranta ta wuce gaba - inda kan taimakawa dubban mutane daga yammacin Afrika warkewa daga tabin hankali.

Domin nuna jin dadi akan gudunmowar da yake bayarwa ta fuskar warkar da masu tabi hankali - a 'yan makonnin da su ka gabata a Abuja, Mr Gregorie ya karbi lambar yabo a matsayin gwarzon shekara na nahiyar Afrika.

Wakiliyar BBC ta Afrika, Leila Adjovi ta yi takakkiya zuwa Benin domin duba kalubalen da yake fuskanta, da kuma yadda ita kanta kasar ke fama da masu lalurar tabin hankalin.