cameroon boko haram
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bam ya halaka mutane 20 a wata kasuwa a Kamaru

'Yan Boko Haram sun kaddamar da hari a cikin garin Meme da ke karamar hukumar Mora a lardin arewa mai nisa a jamhuriyar Kamaru.

Harin ya halaka mutane kusan 20, kuma ya jikkata mutane 52 bisa ga alkaluman da wata jarida mai zaman kanta ta wallafa.

Sai dai har a yanzu gwamnati ba ta tabbatar da wannan lamari ba.

A karo da dama dai garuruwan da suke kusa da kan iyakar Kamaru da Najeriya na fama da hare-hare daban-daban da gwamnati take tabbatar da cewa kungiyar Boko Haram ce take haddasawa.

Ga rahoton da Mohaman Babalala ya aiko mana daga Yaounde.