Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 27/02/2016

Daya daga cikin muhawarar da faduwar farashin mai ta janyo a Nigeria ita ce ta , matakan da suka kamata a dauka domin darajar Naira ta kara karfi ganin yadda ta fadi kasa warwas a 'yan watannin da suka wuce.

Akwai dai masu ra'ayin cewa kamata ya yi gwamnati ta rage darajar Nairar, yayin da wasu ke cewa rage darajar nairar ba lallai ne ta kasance mafita ba.

Ahmad Abba Abdullahi a karo daban-daban ya tattauna da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, da kuma Alhaji Shu'aibu Idris, masanin tattalin arzikin kasa a Nigeria.

Farko Mai martaba Sarki ne ya sake nanata ra'ayinsa na goyon bayan ganin an rage darajar Naira, a matsayinsa na kwararre kan harkar tattalin arzikin kasa .