Juyin Sarauta: Fim kan gudunmawar matan Sarki

Fim din 'Sauyin Sarauta', fim ne kan salon mulki da kuma gudunmawar matan sarki da sauran iyalansa wadanda ke cikin gida a wajen tafiyar da mulki a kasar Hausa kimanin shekara 100 da suka wuce.

Kannywood: Juyin Sarauta
Bayanan hoto,

Fim din 'Sauyin Sarauta', fim ne kan salon mulki da kuma gudunmawar matan sarki da sauran iyalansa wadanda ke cikin gida a wajen tafiyar da mulki a kasar Hausa kimanin shekara 100 da suka wuce.

Bayanan hoto,

A hirar da ta yi da BBC, marubuciya kuma mai shirya fina-finai ta yi takaicin ganin cewa muna barin kyawawan al'adunmu na gargajiya musamman ta bangaren sarauta da kuma irin rawar da mata ke takawa a mulki a gidajen sarakuna.

Bayanan hoto,

Mata da irin rawar da su ke takawa a mulki shi ne jigon 'Sauyin Sarauta' fim din Balaraba Ramat.

Bayanan hoto,

An kashe kimanin naira miliyan goma wajen samar da kayyakin da ake bukata na gargajiyar bahaushe ta dauri a yayin daukar fim din a kauyen Dan Hassan ta jihar Kano.

Bayanan hoto,

Wadanda suka shirya Fim din suna fatan zai ja hankulan masu shekaru da ba kasafai suka fiya kallon fina finan na Hausa ba.

Bayanan hoto,

A wannan makon ne ake sa ran kammala daukar wani fim wanda ya kunshi labarin wata masarautar kasar Hausa.

Bayanan hoto,

Fim din dai ya sha banban da mafi akasarin fina finan Hausa da suke maida hankali kan batun soyayya.

Bayanan hoto,

Wadanda suka shirya Fim din suna fatan zai ja hankulan masu shekaru da ba kasafai suka fiya kallon fina finan na Hausa ba.

Bayanan hoto,

Ana sa ran fim din 'Juyin Sarauta' zai yi kasuwa, saboda za a nuna a gidajen silima a Najeriya