Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane mini hanya 07/03/2016

Hakkin mallakar hoto

Yau kimanin watanni hudu ke nan ana takon saka tsakanin kamfanin samar da layukkan salula mafi girma a Najeriya, wato MTN, da kuma hukumar da ke sa ido kan harkokin sadarwa ta kasar, NCC, kan tarar kudi fiye da Naira Tiriliyan daya da hukumar ta ci kamfanin.

Daga bisani dai gwamnatin Najeriyar ta yi wa kamfanin rangwamen kashi 25 bisa 100 na kudin tarar bayan da ya amsa aikata laifin kin toshe wasu layukansa da ba a yi wa rijista ba. Sai dai kuma duk da haka kamfanin ya kai gwamnatin da hukumar kara a kotu yana korafin cewa ba bi ka'ida ba wajen cin sa tarar amma daga bisani ya janyen karar kuma ya nemi a sasanta lamarin a wajen kotu; har ya biya Naira biliyan hamsin ga hukumar a zaman somin tabi.