macedonia refugees
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Macedonia za ta rufe kofa ga 'yan gudun hijira

Kasar Macedonia ta ce baza ta kara barin 'yan gudun hijira bi ta cikin kasarta daga Girka ba--wanda ke nufin rufe babbar hanyar bi ta cikin kasashen Balkan zuwa arewacin Turai.

Dubban mutane ne suka bi ta Macedonia cikin shekara gudan da ta wuce, amma a 'yan watannin nan kasar na ta sa tsaurara matakai.

Shawarar rufe kan iyakar gaba daya ta biyo bayan sanarwar tsauraran matakai da kasashen Slovania da Serbia da Croatia suka kara dauka.

Kasar Hungary ta ce za ta tura sojoji zuwa bakin katangar da ta gina a kan iyakarta ta kudanci, domin tsaurara tsaro a wajen.

Ga rahoton Haruna Shehu Mararrabar Jos