Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shin me Zuma ya tattauna da gwamnatin Buhari ?

Gwamnatocin Najeriya da Afrika ta Kudu sun rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi fiye da talatin, a fannonin cinikayya da tsaro da makamashi, da dai makamantansu.

An cimma yarjeniyoyin ne a lokacin ganawar da shugaba Jacob Zuma ya yi da takwaransa na Najeriya, Muhammadu Buhari, dazu a Abuja.

A yau ne dai Mr Zuman ya soma ziyarar kwanaki biyu a Najeriyar.

Ga Haruna Shehu Tangaza dauke da karin bayani: