Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An damke 'barayin' shanu 40 a Birnin Gwari

Rundunar tsaron da aka kafa a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta kama wasu da take zargin barayin shanu ne su sama da arba'in, tare da dabbobi kusan dubu biyu.

An kafa rundunar ce domin tabbatar da tsaro da kuma yaki da barayin shanu, da sauran 'yan fashi da makami da masu aikata miyagun laifuka.

Cikin wata hira da abokin aikinmu Ahmed Abba Abdullahi, kwamandan rundunar Operation Yaki Honorobul Yusuf Yakubu Soja, ya ce sun samu nasarar kamawa da kuma kashe wasu daga cikin mutanen ne a aikin samamen da suka fara kwanaki hudu da suka wuce a dajin Birnin Gwari.