barayin shani sun g ta kansu a najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nigeria: Sojoji sun kashe barayin shanu

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarun ayyukan soji da ake yi wa lakabi da 'Operation sharar daji' sun samu nasarar karkashe masu satar shanu a wasu jihohin kasar.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce, a jihar Zamfara ta samu nasarar kashe barayi hudu, ta raunata 16, ta kuma kame uku, sannan kuma ta kwato shanu 486.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, a jihar Katsina rundunar ta kashe barayin shanu biyar, ta kuma kama biyu, sannan ta kwato shanu 116, yayin da soja guda ya samu rauni.

Baya ga wannan, rundunar sojin ta ce, ta lalata sansanonin barayin shanun a jihohin Kaduna da Kano tare da kwato shanu masu yawa.