Syria ceasefire
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tsagaita wuta na aiki a Syria

Mista Kerry ya ce yawan fadan da ake yi a kasar, ya ja baya da kashi casa'in cikin dari.

Wannan dakatarwar ita za ta bayar da damar gudanar da wani zagayen tattaunawa na baya-bayan nan a Geneva, yin hakan ya ci tura a watan jiya.

Babbar kungiyar 'yan adawa ta ce za ta halarci tattaunawar, ba kuma tare da gindaya wani sharadi ba. Sai dai harin da rahotannin ke cewa an kai da jiragen sama a kan fararen hula a Aleppo, ka iya sa shakku a zuciyar 'yan adawa.

'Yar sararawar da aka samu ya ba masu kin jinin gwamnati damar gudanar da zanga-zangar lumana.