maiduguri
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 22 a masallacin Maiduguri

Wasu 'yan kunar bakin wake da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 22, yayin da suke Sallar asuba a wani Masallaci da ke yankin Umarari a kusa da birnin Maiduguri.

Limamin Masallacin, Malam Gwani Kyari ya shaida wa BBC cewa bam din farko ya tashi ne tun kafin su yi raka'ar farko a lokacin Sallar.

Ga rahoton da Raliya Zubairu ta hada mana