sabongari fire outbreak
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana ta kokarin kashe gobarar kasuwar Sabon Gari

A ci gaba da kokarin da ake yi na kashe gobarar, Kwamishinan ciniki da masana'antu na jihar Kano Alhaji Rabiu Bako ya shedawa gidan radiyon jihar cewa, ana yunkurin samar da jiragen sama masu saukar ungulu domin kashe gobarar.

Motocin kashe gobara na gwamnati da na masana'antu masu zaman kan su na ci gaba da yunkurin kashe gobarar.

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce ta tura sama da jami'anta 500 dan samar da tsaro a kasuwar har yanzu dai wutar na ci gaba da ci.

Bayanai dai na cewa gobarar ta tashi ne tun tsakar daren jiya, kuma har yanzu tana ci ba a kai ga kashe ta ba.