Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bulaguro mai cike da hadari

A bana, mutane fiye da 13,000 ne suka yi nasarar tsallake Bahar Rum domin shiga Italiya daga arewacin Afrika, mmma ruwa ya ci wasu karin dubbai.

Kafin wadannan 'yan ci rani su kai ga shiga jiragen ruwa a gabar ruwan Libya, da dama daga cikinsu su kan kwashe har kwanaki shida ana tafiya da su cikin mota a hamadar sahara cikin matsanancin zafi.

Garin agadez na arewacin Nijar nan ne inda 'yan ci ranin ke yada zango a kan hanyarsu ta zuwa Turai.