Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 02/04/2016

A Nigeria gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El Rufai ya yi bayani a bisa wasu al'amurra da suka haifar da cece-kuce a fadin jahar.

Gwamnan wanda ya gana da manema labarai, yayi bayani dangane da rikicin gwamnatin jihar da 'yan kungiyar kwadago NLC, da batun rikicin nan da mazauna wata unguwa mai suna Bagyi Villa da gwamnati da kuma batun dokar da gwamnatin jihar ta bullo da ita domin sa ido akan yadda harkokin addini zasu gudana a jihar.

Wannan ne dai karo na farko da gwamnan ya yi bayani a bisa al'amurra da dama da suka shafi jahar har ake ta cece-kuce a kai.

Wakilinmu na Kaduna Nurah Mohammed Ringim ya tattauna da gwamnan, inda ya soma da tambayarsa ko wadanne kalubale ne ke fuskantarsa tun soma mulkin jihar: