Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shirin Sanin kai: Mata a wuraren gyaran gashi

Shirin Sanin kai na BBC na 2016 ya yi duba kan yadda mata suka mayar da wuraren gyaran gashi wajen tattauna al'amuran da suka shafesu, da kuma yadda suke kallon kansu.

Nan wajen gyaran gashi ne da ya zama wani dandali na tattaunawa kan sanin kai da kuma nuna kamannin mata a duniya.

A gabashin London, wata 'yar Kamaru mai suna Cece ta bayyana wa Pearl mai gyaran gashi dalilin da yasa take son yanayin gyaran gashinta ya nuna cewa ita 'yar Afrika ce. Amma akwai wani salo da ake mata na yadda gashinta zai zamo ainihin yadda yake.