Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayoyin 'yan Nigeria kan 'yan matan Chibok

A ranar Alhamis ne 'yan matan makarantar sakandare ta garin Chibok da ke jihar Borno suka cika shekara biyu a hannun mayakan Boko Haram, kuma har yau ba a ji duriyarsu ba.

Mayakan sun sace 'yan matan sama da 200 ne ranar 14 ga watan Afrilun 2014 da daddare a makarantarsu.

BBC ta ji ra'ayoyin wasu 'yan Najeriya a kan ko suna da wani fata kan dawowar yaran?