Hira da ministar kudin Nigeria kan tattalin arziki

Mutane da dama sun jima suna jira su ji me ministar kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun, za ta shaida wa cibiyoyi masu ba da rance na duniya don su tallafa wa kasarta.

To a kwanan nan ta tattauna da Asusun bada Lamuni na Duniya, IMF, da Bankin Duniya, da kuma Bankin Raya kasashen Afirka.

Wakiliyar BBC, Lerato Mbele ta tattauna da ita don jin yadda wadannan cibiyoyi na duniya suka karbi sakonta.