Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 30/04/2016

Satar mutanen don neman kudin fansa na kara zama wata babbar matsalar tsaro a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ke kara jefa rayuwar mazauna yankunan cikin fargaba.

Matsalar dai ta fi kamari ne a kudancin jihar da ke makwabtaka da dajin Falgore wanda ke hade da wasu manyan dazuzzuka a yammacin Afrika, dazukan da kuma suka zama tamkar matattara ga masu aikata miyagun laifuffuka.

Baya ga Jihar Kano, jihar Kaduna ma na fuskantar wannan matsala, lamarin da ya sa a farkon wannan watan babban sipeton 'yan sanda Najeriyar ya umurci mataimakin shugaban 'yan sanda AIG na shiyya ta 7 AIG da ya koma Kaduna har sai al'amurran tsaro sun inganta a jihar.

A filin Gane mani Hanya na wannan makon, wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya hada mana rahoto na musamman kan yadda matsalar ta ke kara kamari a Jihar Kano da kuma abinda hukumomi suke yi don magance ta.