Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taron shugabannin Afrika kan kare giwaye

Shugabannin siyasa da na kungiyoyin kare namun daji sun yi wani taro a Kenya inda suka tattauna kan lalubo hanyoyin da suka fi dacewa na kare giwaye daga masu farautarsu, wadanda ke dauke da muggan makamai.

Dubban giwaye ne ake kashewa a kowacce shekara domin a samu haurensu, saboda ana bukatarsa sosai a China da Hong Kong.

To sai dai duk da cewa an haramta cinikin hauren giwar, har yanzu ana cigaba da sayar da shi ba bisa ka'ida ba, a shaguna da dama na Asiya.

Ga rahoton daa Jimeh Saleh ya hada.