Hanyoyi hudu da CIA ke katsalanda a Afrika

Hakkin mallakar hoto B
Image caption An tsare Nelson Mandela a 1962 kuma daga baya aka yanke masa hukunci bisa yunkurin kifar da gwamnati.

Hukumar leƙen asiri ta Amurka CIA, na da dogon tarihin yadda take shiga al'amuran nahiyar Afrika, don haka rahotannin da jaridar Sunday ta bayar cewa an kama Nelson Mandela ne a shekarar 1962, sakamakon labarin da hukumar CIA ta bayar, bai zo da mamaki sosai ba.

Yawancin al'amuran sun faru ne a lokacin yaƙin cacar baka, sakamakon ƙoƙarin da Amurka da Rasha ke yi na samun gindin zama a nahiyar.

Ayyukan sirri da CIA ke gudanarwa, al'amura ne waɗanda da wuya a iya gane kansu.

Amma binciken da ake yi kan aikin hukumar, da kuma labaran da ake samu daga bakin tsoffin ma'aikatanta, sun tona abubuwa da dama kan yadda hukumar ke ƙoƙarin yin katsalandan a al'amura da dama.

Ga wasu misalai guda huɗu:

1. 1961 - Kisan gillar da aka yi wa Patrice Lumumba a Congo

Hakkin mallakar hoto AFP

Patrice Lumumba shi ne firaiminista na farko na ƙasar Congo, bayan samun mulkin kanta a shekarar 1960, amma watanni ƙalilan kawai ya yi a kan mulkin, kafin a hamɓarar da shi tare da kashe shi a watan Janairun 1961.

A shekarar 2002 ne ƙasar Belgium wadda ita ce ta reni Congo, ta ɗauki alhakin hannu a kisan nasa, amma Amurka ba ta taɓa furta rawar da ta taka kan hakan ba, duk da cewa an daɗe ana zarginta.

Shugaban Amurka, Dwight D Eisenhower, ya damu a kan kwaminisanci, sannan kuma bai ji daɗin abin da ya faru a Congo ba sakamakon irinsa da ya faru a Cuba.

A cewar wata magana da aka rubuta a littafin 'Death in the Congo,' wanda aka rubuta kan kisan gillar da aka yi, ''shugaba Eisenhower ne ya bayar da umarnin kashe Lumumba. Ba a yi wata tattaunawa ba, kawai sai aka cigaba da taron ƙAsa kan tsaro.''

Wani babban jami'in gwamnati a wancan lokaci Lawrence Devlin, ya shaida wa BBC a shekarar 2000cewa, ''Amma ba a samu damar aiwatar da wani shiri da CIA ta yi da nufin sanya guba cikin man goge bakin Lumumba ba.''

Duk da cewa babu shakka CIA ta so kashe Lumumba, binciken bai nuna akwai sa hannun Amurka, kai tsaye, a samun nasarar kisan da aka yi masa daga karshe.

2) 1965 - Hamɓare Kwame Nkrumah a Ghana

Hakkin mallakar hoto EVENING STANDARD

A 1966 ne aka yi wa shugaban kasar Ghana na farko, Kwameh Nkrumah juyin mulki, a lokacin da ya fita kasar waje.

Kuma daga baya ya fahimci cewar Amurka na da hannun a hamɓararwar da aka yi masa, sannan tsohon jami'in tattara bayanan sirri na CIA, John Stockwell, ya tabbatar da wannan batun a wani littafi da aka wallafa a 1978.

A littafin mai suna In Search of Enemies, John Stockwell ya rubuta " jami'an CIA na birnin Accra sun samu goyon bayan hedikwatar CIA wajen kusantar 'yan tawaye.

" An ba su isassun kudade kuma sun aiki tare da wadanda suka shirya juyin mulkin har suka cimma burinsu."

Ya ce jami'an CIA a Ghana sun shiga al'amarin dumu-dumu kuma "an yabawa jami'anta bisa samun nasarar juyin mulkin."

Wasu takardun da ba na sirri ba na gwamnatin Amurka sun nuna cewa Amurka tana da masaniyar afkuwar juyin mulkin, sai dai kuma takardun ba su fayyace ko akwai goyon bayan wani jami'in gwamnatin ba.

Har wa yau, wasu karin takardun da aka rubuta bayan juyin mulkin, sun bayyana tumbuke Kwameh Nkrumah a matsayin "wata nasara babba. Nkrumah yana kokarin dakile burinmu fiye da duk wani bakin mutum."

3) 1970s - nuna kin jinin MPLA a Angola

Hakkin mallakar hoto AFP

A Angola, kungiyoyi uku ne suka yi fafitika ta neman ikon kasar, bayan samun 'yancin kai, a 1975, daga kasar Portugal. A lokacin dai kungiyar MPLA wadda Agostinho Neto ya jagoranta ta karbi ikon Luanda, babban birnin kasar.

Jami'in hukumar CIA na farin kaya a Angola, a 1975, Mista Stockwell ya rubuta cewa Amurka ta kudiri niyyar nuna adawa da MPLA, saboda ana yi mata kallon tana da kusanci da tarayyar Rasha ta wancan lokacin, a inda Amurkar ta marawa kungiyar FNLA da Unita, duk kuwa da cewa su ma kungiyoyin biyu suna samun tallafi daga tarayyar ta Rasha.

A wani shirin talbijin, Mista Stockwell ya fadi cewa CIA ta taimaka a asirce wajen shigar da makamai cikin kasar da suka hada da kananan bindigogi 30,000, ta makwabciyar kasar, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango.

Mista Stockwell, ya kara da cewa jami'an CIA sun kuma horas da mayaka.

Wasu takardun da ba na sirri ba mallakar gwamnatin Amurka da suka yi cikakken bayani kan tattaunawa tsakanin shugaban CIA da sakataren harkokin wajen Amurka tare da wasu, sun nuna yadda CIA ta ba wa wadanda suka yaki kungiyar MPLA.

4) 1982 - Tallafawa Hissene Habre a Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP

Hissene Habre bai yi nasara ba a yunkurinsa na kwace mulki da karfin tuwo, a 1980, a Chadi.

Amma kuma yunkurinsa ya janyo shugaban lokacin,Goukouni Oueddei, ya nemi taimakon shugaban Libya, Muammar Gaddafi, a inda sojojinsa suka fatattaki Habre har ma ya yi gudun hijra.

Yunkurin hadin gwiwa tsakanin Libya da Chadi bai yi wa Amurka dadi ba, musamman a lokacin da aka fara yi wa Gaddafi kallon mai adawa da tsare-tsaren Amurka.

A wata mujalla, Michael Bronner, ya rubuta cewa darektan CIA, tare da sakataren harkokin waje " yana ta'allake da batun fara yakin sunkuru a Chadi, bisa hadin kan Habre."

An yi zargin cewa Amurka ce ta marawa Habre baya ya hambarar da shugaban kasar a 1982, ta kuma taimaka masa a iya tsawon lokacin mulkin kama-karyar da ya yi.