Murnar samun 'yancin kai a Somaliland

Mary Harper, editar Afirka ta BBC ce ta rubuta.

Image caption Murnar samun 'yancin kai a Hargeisa, babban birnin yankin Somaliland

Bayan mummunan yaƙin basasa shekara 25 a Somaliya, arewa maso yammacin ƙasar ya ɓangare daga sauran sassanta , a inda ya zama ƙasa mai cin gashin kanta.

Kuma har yanzu, babu wata ƙasa guda ɗaya da ta amince da ƙasar ta Somaliland. To amma yankin mai al'umma kimanin miliyan 3.5, na daya daga cikin yankunan da suke da tsayayyiyar dimokradiyya a kusurwar nahiyar Afirka.

A BBC, ba ma kiran ƙasar Somaliland da ƙasa saboda ba ta zamo ƙasa a hukumance. Muna kiranta da "jamhuriyar mai iƙirarin 'yancin kai", abin da 'yan Somaliland din da dama ke suka.

To sai dai yankin yana da irin kudinsa daban da Fasfo da sojoji da kuma tsarin shari'a. Shugaban kasar yankin ya hau mulki ne sakamakon zaben da aka fafata sosai, a inda ya dara abokin hamayyarsa da kuri'u kalilan. Sabanin sauran kasashen Afirka, ana amincewa da sakamakon zabe a yankin, ko da kuwa jam'iyyar adawa ce ta yi nasara.

Yankin na Somaliland dai yana da nasa 'yan matsalolin. Ana takaddama a kan mafi yawancin sassan gabashin yankin na Somaliland da sauran shiyyoyi. Al'ummar shiyyar yammaci su ma suna fafitikar neman samun 'yancin gashin kai. Akwai kuma rahotanni da ke nuna cewa akwai daidaikun 'yan kungiyar al-Shabab.

Image caption Lokacin 'yancin kai a yankin Somaliland
Image caption Hawan rakuma a lokacin bikin murnar 'yancin kai

Wasu 'yan ciranin da suka mutu a Bahar Rum, 'yan yankin na Somaliland ne, a inda aka kiyasta cewa kaso 75 na matsan yankin suna fama da rashin aikin yi.

Yayin wata ziyara da na kai yankin, na ga sahun matasa suna tafiya a bakin tituna dauke da kananan jakunkuna. An fada min cewa " suna kan Tahrib," wato suna kan hanyarsu ta tafiya turai ko kuma yankin Gulf.

Hukumomin a yankin na Somaliland suna da tsauri a kan aikin jarida, a inda wani lokaci suke tsare 'yan jarida da kuma rufe gidajen jaridu. A watan Janairu, an zartar da hukuncin kisa kan wasu masu zaman gidan kaso guda shida da aka samu da laifin kisan kai.

Irin wadannan matsalolin ne kasar Somaliya ta asali take fuskanta, a inda ko a bara sai da wasu mutane hudu 'yan Somaliya suka fuskanci dauri, bayan da suka dawo yankin Somaliland daga Somaliya. Laifin da ake zargin su da shi shi ne kada tutar Somaliya mai launin zargina, a lokacin gasar rawa a babban birnin kasar, Mogadishu. Ita da Somaliland tana da tata tutar mai launin kore da fari da ja. 'Yan yankin na Somaliland suna alfahari da su damkawa duk wani jami'in huldar jakadancin wata kasa da ya zo yankin nasu, tutar, a inda wasu lokuta jami'an ke nuna rashin jin dadi da zarar an warware tutocin a gabansu saboda hakan na sanya su cikin wani yanayi na tsaka mai wuya, sakamakon rashin amincewar kasashen duniya kan kasancewar yankin kasa mai cin gashin kanta.

Zaman lafiya

Maiyiwuwa ne ace akwai kwarya-kwaryar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na Somaliland. Wani lokaci, na kan yi kai na komo tsakanin kasar Somalia da yankin Somaliland, a rana daya, kuma ba na ganin wani babban banbanci tsakaninsu. A kasar Somaliya, a matsayina na 'yar jarida daga turai, ba na iya sakewa na zagaya a kasar, ba tare da jami'an tsaron guda shida ba da za su ba ni kariya, wadanda suke cikin shirin ko-ta-kwana. Muna zagayawa ne a cikin motoci guda biyu, a inda nake makalewa a jikin tagar motar mai duhun da wanda ke waje ba ya ganin na ciki. A lokacin da nake a Mogadishu, mafi yawancin lokuta akan samu hare-haren kunar-bakin-wake da hare-haren gurneti da kuma na motocin yaki.

A yankin Somaliland kuwa, ina zuwa duk wurin da nake so, ni kadai, koda kuwa da daddare ne. 'Yan kasar Somali da dama ma na yin amfani da wannan damar ta zaman lafiya, musamman a lokacin bazara, lokacin da yankin na Somaliland yake zama wani wurin shakatawa ga mutanen Somaliya daga ko ina a fadin duniya. Iyalai masu yawa 'yan asalin Somaliya daga Amurka da Canada da yankin Turai da Australia da yankin Gulf da ma sauran sassan duniya, suna tuttuda zuwa yankin na Somaliland domin yin hutawa.

Image caption Hoton jirgin da Rasha ta yi amfani da shi a lokacin yakin basasa, ya zama kayan tarihi.

Iyaye suna nunawa 'ya'yansu yanayin rayuwar 'yan Somaliya na gargajiya, wasu lokutan ma sukan dauke su zuwa daji domin ganin irin rayuwar 'yan Somali makiyaya. Maza na shan nonon rakumi da namansa. 'Yan matan Somali wadanda suke a kasashen waje na zuwa dakunan kwalliya domin ganin yadda ake zanen kunshi a hannu da kafa. Ana kuma samun yaukakar soyayya tsakanin matasan ma'aurata, a inda suke musayar askirin, a asirce.

Image caption Saye da sayarwa na tafiya a wurin kama kifi na garin Berbera

A duk lokacin da aka yi batun banbanci tsakanin kasar Somalia da yankin Somaliland, tambayar da ke fara zuwa ran mutane ita ce wacce ce aka duniya ta aminta a matsayin kasa?

Somaliya dai kasa ce wadda kowa ya yarda da kasancewarta. An kashe biliyoyin daloli wajen sake gina kasar da ta yi fama da rikicin na fiye da shekara 25. Akwai dai alamun samun cigaba amma kuma babu alamun cewa cikakken zaman lafiya zai dawo a nan kusa.

Shi kuma yankin Somaliland bai samu amincewa ba, a matsayin kasa mai cin gashin kanta daga kasashen duniya, kuma ba ta samun tallafi daga kasashen ketare. Amma dai yankin ya yi kokarin sake gina Somaliland din domin farfadowa daga radadin yakin basasa da suka yi fama da shi.

Image caption Taswirar yankin Somaliland

A farkon shekarar 1990 ne dai na fara kai ziyara zuwa yankin Somaliland, a lokacin da babu komai a babban birnin yankin, Hargeisa, illa ɓuraguzai . A lokacin kuma da na koma a shekarar 2011, na tsaya a kan wani tsauni, na yi mamakin irin cigaban da na gani a birnin.

Alamu dai na nuna cewa zai yi wuya duniya ta amince da kasancewar yankin na Somaliland a matsayin kasa mai cin gashin kai. To amma abin tambaya a nan shi ne idan yankin ya samu 'yancin kai, shin ko su ma 'yan kasar za su fada cikin halin yaki kamar yadda kasar Somaliya ta samu kanta a ciki?