Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar karancin tumatur a Nigeria

Manoman rani a Najeriya sun ce sun fuskanci mummunan asarar tumatur, sakamakon wata tsutsa da ke cinye tumatur din a lokacin da yake gona.

Matsalar ta haifar da karancin tumatur da tsadarsa a Najeriya, inda yanzu haka kwando daya ya kai dubban nairori.

A jihar Kaduna ma har gwamnati ta ayyana dokar ta baci a kan noman tumatur.

Ga rahoton Yusuf Yakasai daga Kano: