Wani dalibin Nigeria a Birtaniya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Faduwar Naira ta jefa daliban Nigeria cikin kunci

Faduwar darajar Naira ta saka daliban Nigeria da dama dake karatu a Birtaniya cikin mawuyacin hali.

Daliban na alakanta wannan lamari da matakan tattalin arzikin da gwamantin Shugaba Muhammadu Buhari ke dauka musamman wadanda suka shafi musayar kudaden ketare.

A yanzu adadin daliban da ke fita karatu kasashen waje ya ragu matuka tun bayan da Mr Buhari ya hau karagar mulki.

Jimeh Saleh ya zanta da wasunsu da suka ce karatun ma na neman gagararsu.