Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 04/06/2016

Farashin man fetur na cigaba da faduwa a kasuwannin duniya, abin da ya jefa tattalin arzikin kasashe masu arzikin man, kamar Najeriya cikin mawuyacin hali.

Masana sun ce babu mamaki farashin ya cigaba da faduwa saboda wasu nau'o'in makashin da ake cigaba da ganowa da kuma karin kasashen da ke gano man.

Dokta Mas'ud Ibrahim malami ne a jami'ar Coventry dake Ingila, kuma kwararre a kan kungiyar OPEC din wadda daya daga cikin manufofinta shine daidaita farashin man domin amfanar mambobinta.

Jimeh Saleh ya fara da tambayar sa ko menene humimancin kasashe su cigaba da zama a cikin kungiyar ta OPEC ganin cewa farashin man na ta faduwa?