Dakarun Libya sun kwace tashar ruwan Sirte

Dakarun Libya masu goyon bayan gwamnatin hadaka da ke birnin Tripoli sun kwace iko da tashar jirgin ruwa da ke birnin Sirte, bayan fafatawa da mayakan IS.

A watan jiya ne dai aka fara gumurzun neman iko da birnin tsakanin mayakan gwamnatin da na kungiyar IS.

Birnin na Sirte ya kasance wurin da dakarun IS suke da karfi, bayan Syria da Iraqi.

Galibi dakarun masu goyon bayan gwamnatin hadakar, sojojin sa-kai ne da suka fito daga yamamcin birnin Misrata.

Mai magana da yawun dakarun General Muhammad al-Ghusri, shugabanni mayakan na IS sun tsere zuwa cikin hamada a kudancin kasar.

Amma ya kara da cewa akasarin mayakan I-S din an yi musu kofar rago a tsakiyar birnin Sirte, kana ana cigaba da kai farmaki.