Yadda sanatoci suka yi ɓaɓatu kan Buhari

Daya daga cikin 'yan majalisar dattawan Najeriya, Dino Melaye, ya shaida wa BBC cewa ba su da niyyar tsige shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Sanata Melaye ya kuma musanta zargin da aka yi cewa ya yi barazanar yi wa matar Sanata Bola Tinubu, Remi Tinubu, ciki.

Ku saurari cikakkiyar hirarmu da shi kan yadda zaman majalisar dattawan na sirri ya kaya: