Hotunan kaddamar da jirgin kasa mafi gudu a Nigeria

Shugaban Najeriya ya kaddamar da jirgin kasa mafi gudu wanda ba a taba yin irinsa ba a kasar. Abokin aikinmu Haruna Tangaza ya bi tawagar shugaban a cikin jirgin, kuma shi ya dauko mana hotunan.

Jirgin kasa mafi gudu
Bayanan hoto,

Tun lokacin mulkin Cif Olusegun Obasanjo aka fara shirin samar da wannan jirgi domin ciyar da kasar gaba.

Bayanan hoto,

Jirgin zai dinga zirga-zirga ne tsakanin biranen Abuja da Kaduna, kuma duk wanda zai hau shi zai biya Naira 500.

Bayanan hoto,

Jirgin yana daukar fasinjoji dari biyar.

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari da ministan sufuri Rotimi Ameachi da ministan birnin Abuja na daga cikin mutanen da suka shiga jirgin a yayin kaddamarwar.

Bayanan hoto,

Jirgin zai dinga tafiyar tsawon sa'o'i biyu ne daga Abuja zuwa Kaduna, ko daga Kaduna zuwa Abuja.

Bayanan hoto,

Wani kamfanin kasar China ne ya yi aikin samar da jirgin, kuma tun lokacin mulkin Goodluck Jonathan aka fara aikin.

Bayanan hoto,

Sai dai aikin bai kammala ba sai a yanzu, dalilin da yasa shugaba Buhari ya kaddamar da fara aikinsa kenan.

Bayanan hoto,

An kawata jirgin da kujerun jirgi na zamani da makewayi da sauran abubuwan ban sha'awa.

Bayanan hoto,

Jam'iyyar adawa ta PDP wadda ita ce ta tsohon shugaba Jonathan ta yi ta wallafawa a shafinta na Twitter cewa a karkashin mulkinta ne aka yi wannan ''hobbasa''.

Asalin hoton, APC Nigeria

Bayanan hoto,

Wannan ministan harkokin sufurin Najeriya ne Mista Rotimi Ameachi a yayin da ya shiga jirgin.

Bayanan hoto,

A tashin farko da ya yi yayin kaddamarwar, jirgin ya tashi ne daga tashar Idu da ke birnin Abuja.

Asalin hoton, APC Nigeria

Bayanan hoto,

Sai kuma ya tsaya a tashar Kubwa duk dai a birnin Abujan, cikin tafiyar minti 18.

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya sauka ne a tashar Kubwa, inda jirgin kuma ya cigaba da tafiya zuwa birnin Kaduna.

Bayanan hoto,

Wannan jirgi dai shi ne irinsa na farko mafi gudu da aka kaddamar a Najeriya, kuma a yanzu zirga-zirgarsa za ta tsaya ne tsakanin Abuja da Kaduna.