Rayuwar miliyoyin mutane a kasashen da ke kewayen tafkin Chadi ta dogara ne kan kamun kifi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: Matsalolin kamun kifi a Najeriya

A shirinmu na wannan makon Bilkisu Babangida ta yi hira ne da shugaban masu sana'ar kifi a Najeriya, Mr Anthony A Ashagye kan matsalolin da suke fuskanta.

Ya bayyana mata irin matsolin da masu sana'ar ke fuskanta a Najeriya saboda tashin hankali na 'yan Boko Haram da kuma malalar mai a yankin Niger Delta.