Awon jikinka/ki ya zo daya da ɗan wasan Olympic?

Manhajarka/ki ba ta aiki da wannan tsarin Ku karanta labaran BBC kan Rio 2016 a nan

Ta yaya aka gane wanda kuka zo daya?

An yi amfani da 'yan wasan motsa jiki fiye da 10,000 cikin sama da 11,550 a wannan aikin. Ba a sanya 'yan wasa 1,500 ba ne saboda babu bayanai kan tsawo da nauyi da kuma shekarunsu. Kuma an samu bayanan ne daga hukumar tattara bayanai ta Olympic.

An kuma yi amfani da wani salon lissafi da ake kira Euclidean distance wajen daidaita bayananka da na dan wasa. Lissafin na ba da damar tattara bayanai dag nesa tsakanin masu amfani da kuma na duka 'yan wasa. An samu bayanan ne daga ODF kuma bayanan sahihai ne har ranar takwas ga watan Agusta 2016.

Ana hada ɗan wasan da ya fi kusa da tsawo da kuma nauyin mai amfani da wannan manhaja. Idan kuma aka samu 'yan wasa fiye da uku da suka fi kusa da mutum sai a yi amfani da ranar haihuwarka/ki.


Majiyoyi

Nassos Stylianou da John Walton da kuma Nathan Mercer ne suka shirya wannan bayanai. Ransome Mpini ya yi fashin baƙin bayanan, Gerry Fletcher da Luke Ewer da Chris Ashton ne suka tsara. Yayin da Liam Bolton da Phil Dawkes suka kara yin aiki a kai.

Labarai masu alaka