Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko Dogara yana kuka sai ya sauka - Jibrin

Tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Najeriya, Abdulmumini Jibrin, ya ce dole ne kakakin majalisar ya sauka daga mukaminsa ko yana kuka ko yana murna.

Yakubu Dogara da sauran shugabannin majaliasar na fuskantar matsin lamba kan zargin yin cushe a kasafin kudin kasar na bana.

A ranar Laraba ne hukumar da yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta fara gudanar da bincike kan zargin, wanda Mista Jibrin ya gabatar mata, bayan da aka kore shi daga shugabancin kwamitin kasafin kudin.

Mista Dogara da sauran shugabannin majalisar sun yi watsi da zargin da ake yi musu, suna masu cewa ba su sabawa doka ba.

Mista Jibrin ya shaida wa Yusuf Yakasai cewa ya yi farin ciki da matakin na EFCC.

Labarai masu alaka