Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An fara tantance zawarawa a kano

A Kano, ana cigaba da aikin tantance zawarawa a wani bangare na shirin auren zawarawa da gwamnatin jihar ke daukar nauyi.

A baya dai, gwamnatin jihar Kano ta aurar da dubban 'yan mata da zawarawa a karkashin wannan shiri, wanda ake ganin ya samu tagomashi saboda matakai da sharuddan da ake gindayawa kafin yin saki, idan an yi auren.

Su dai, hukumomi suna cewa sun bullo da shirin ne da nufin rage baɗala saboda rashin aure.

Wakilinmu na Kano Mukhtari Adamu Bawa ya ziyarci inda ake aikin tantancewar ga kuma abin da ya tsakuro mana:

Labarai masu alaka