Baraka a jamiyyar PSP dake Najeriya

Taswirar Najeriya
Image caption Akwai sama da jamiyyun siyasa hamsin a Najeriya

A Nigeria wani rikici ne ya kunno kai a cikin jam'iyyar PSP, inda wasu`yan majalisar zartarwar jam'iyyar suka ce sun rushe shugabancin jam'iyyar na kasa karkashin jagorancin Dr Junaidu Muhammad da sakatare da kuma mataimakinsa na kasa.

Su dai masu daukan wannan mataki sun bayyana cewa sun rushe shugabancin ne sakamakon rashin kiran taron jam'iyyar duk bayan watanni uku uku, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada, da kuma rashin cikakken bayanin matsayin asusun jam'iyyar tun bayan da aka zabe su a watan Disambar 2006.

Kuma tuni suka ce sun nada Tank Kenmi tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar a matsayin shugaban riko, wadanda aka basu wata daya su shirya babban taron jam'iyyar.